Karon iyalan Kate da 'yan jaridun Burtaniya

Kate Middleton Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Kate Middleton da 'yan uwanta suna jan hankalin jama'a

Iyalan Kate Middleton sun kai korafi ga ofishin karbar koke na 'yan jaridar Burtaniya (PCC), kan zargin muzguna musu da wasu masu daukar hoto suka yi.

BBC ta fahimci cewa lamarin ya faru ne lokacin da masu daukar hoto na kamfanonin dillancin labarai suka bi mahaifiyar Kate Middleton da 'yar uwarta.

Kungiyar sa'ido kan 'yan jaridu a Burtaniya, ta aika sako ga editoci tana mai gargadinsu abisa la'akari da ka'idojin aikinsu.

Wakilin BBC kan harkokin gidan Sarautar Burtaniya Peter Hunt, ya ce masu daukar hoto sun bi Carole Middleton da 'yarta Pippa a kafa.

Ka'idojin aikin jarida a Burtaniya dai sun bayyana cewa: "Bai kamata 'yan jarida su yi wani abu da zai muzgunawa mutane ba, ko kuma matsa lamba wajen neman abu."

Sai dai mai magana da yawun fadar St James's Palace ya ce: "Babu wani korafi a hukumance da iyalan Middleton suka gabatar ga ofishin na PCC kan kaucewa ka'idar aikin jarida.

"Amma bayan faruwar wani lamari kan zargin muzgunawa da kuma takurawa daga wasu 'yan jarida masu zaman kansu da kuma na kamfanonin dillancin labarai, iyalin Middleton, ta hanyar ofishin PCC, suna son jawo hankalin editoci kan lamarin.

Mai maganar ya kara da cewa za su dauki mataki "mai tsauri" idan wani kamfanin daukar hoto ya kara tunkara ko kuma muzguna musu.