Ziyarar William da Kate zuwa Lancashire

Ziyarar William da Kate zuwa Lancashire Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption William da Kate sun samu tarba ta musamman a Lancashire

Yarima William da amaryarsa Kate Middleton sun samu tarba ta musamman daga dubban jama'a da suka yi musu maraba a Lancashire a bayyanarsu ta karshe a bainar jama'a kafin bikin.

Masoyan biyu sun samu tarba daga kusan mutane 15,000 wadanda suka zo domin ganinsu a Witton Country Park da ke Blackburn a Yammacin Litinin.

Tun da farko sai da suka ziyarci makarantar Darwen Aldridge Community Academy, inda Yarima William ya bude sabuwar makarantar.

An tafka ruwa sosai wanda ya hana jama'a fitowa, amma duk da haka jama'a sun yi wa masosan biyu maraba lokacin da suka isa.

Yarima Willliam ne ya bude fagen, ta hanyar daga wa jama'a hannu.

Sai dai ruwan ya dauke lokacin da Yariman da masoyiyarsa suka isa dandalin wasanni na Pavilion a Witton Country Park.

Sun gaida manyan bakin da suka halarci wurin sannan suka hau layi a daya bangaren domin shiga tseren gudu, inda jama'a da dama suka kalle su.

Sai dai Natalie Sailor, 'yar shekara 16, daga Lancaster, ita ce ta lashe tseren, kuma masoyan biyu sun bata kyauta domin murnar ziyarar ta su.