Jega ya ce Dr Goodluck ne ya lashe zabe

Wasu masu zanga zanga a Kano Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Wasu masu zanga zanga kan sakamakon zabe a Kano

Shugaban Hukumar zaben Nigeria, INEC, Parfesa Attahiru Jega ya bada sanarwar cewa shugaba mai ci, Goodluck Jonathan ya samu kusan kuru'u miliyan 23 yayinda babban abokin takararsa, Janar Muhammadu Buhari ya samu kuru'u fiye da miliyan 12 a zaben shugaban kasar da aka yi a ranar Asabar.

Hakan dai ya tabbatar da Mr Jonathan a matsayin wanda ya lashe zaben.

Tun farko kuma shugaba Goodluck Jonathan ya yi kira ga shugabannin siyasa da su kwantar da hankalin magoya bayansu, sakamakon tashin hankalin da ya barke a sassa da dama na Arewacin kasar.

Mr Jonathan ya fitar da wata sanarwa inda ya yi kira ga abokan takararsa da su taimaka wajen hana bazuwar tashin hankalin.

Tashin hankalin dai yayi sanadiyar asarar rayuka , da kuma kona gidajen wasu kusoshin 'yan arewacin Nijeriya da ake dangantawa da jam'iyyar PDP mai mulki.