INEC ta ce duk mai wani korafi yana iya zuwa kotu

Shugaban INEC, Parfesa Attahiru Jega
Image caption Shugaban INEC, Parfesa Attahiru Jega

A Najeriya, Hukumar zaben kasar ta ce babu wani abin da za ta yi wa jam`iyyun adawar da ke korafi game da sakamakon zaben shugaban kasar, wanda ya ayyana shugaba Goodluck Jonathan a matsayin wanda ya lashe shi.

Hukumar ta shawarci duk mai korafi ya garzaya zuwa kotu saboda ta ce da zarar an sanar da sakamakon zabe, to kuwa ba ta da sauran iko kansa.

Hukumar zaben dai tana maida martani ne ga korafin da jam`iyyar adawa ta CPC ta gabatar ma ta lokacin da take tattara sakamakon zaben shugaban kasar a jiya.

Jam`iyyar ta CPC dai ta yi zargin cewa an tabka magudi a wasu sassan kasar a lokacin zaben.