Birtaniya zata tura jami'ai zuwa Bengazi

Gwamnatin Biritaniya za ta tura wata tawagar soji ta ba da shawara zuwa birnin Benghazi na gabacin Libya, inda 'yan adawa suke da karfi.

Sakataren waje na Biritaniya, William Hague, ya ce ba za su shiga cikin horar da dakarun da ke gaba da Kanar Gaddafi ba, amma za su ba su shawara a kan yadda za su inganta dabarunsu na yaki.

Wakilin BBC ya ce, tuni da ma akwai tawagar Biritaniya ta difilomasiya a yankin Bengahazi da 'yan adawa ke da karfi.

Yanzu kuma gwamnati ta yanke shawrar aikawa da abinda ta kira dakarun da za su dinga ba da shawara.