Mutane fiye da dubu arba'in suka bar gidajensu a rikicin Najeriya

Kungiyar agaji ta Red Cross reshen Najeriya ta ce adadin mutanen da suka tsere daga gidajensu a sanadiyar rikicin da ya biyo bayan zaben shugaban kasa, sun kai dubu Arba'in da takwas.

Wannan adadin dai ya ninka wanda kungiyar Red Cross din ta bayyana a jiya Talata.

Haka nan kuma kungiyar ta Red Cross ta ce mutane dubu 8 da dari biyar ne suka bar gidajensu a Anacha ta jihar Anambra zuwa barikokin soji.