An zabi Hama Amadou sabon kakakin majalisar dokokin Nijar

Shugaban Nijar Mahamadou Issoufou
Image caption An kammala zaben kakakin majalisar dokokin kasar Nijar inda 'yan majalisar dokokin suka zabi Malam Hama Amadou a matsayin sabon kakakin majalisar

'Yan majalisar dokokin kasar Nijar sun zabi Alhaji Hama Amadou, shugaban jam'iyyar Moden Lumana Africa, wani tsohon Fira Minista a matsayin kakakin majalisar dokokin kasar.

Malam Hama Amadou dai ya kasance shugaban jam'iyya ta biyu mafi girma a cikin kawancen wasu jam'iyyu 34 wadanda suka kulla kawance da jam'iyyar PNDS Tarayya da ta dora Alhaji Mahamadou Isooufou a matsayin sabon shugaban kasar Niger a kan karagar mulki bayan da aka gudanar da zagaye na biyu na zaben shugaban kasa a watan Maris da ya gabata

Malam Hama Amadou ya samu kuri'u 103, kuma ana saran zai jagoranci majalisar dokokin harna tsawon shekaru biyar

Wasu 'yan Nijar dai sun bayyana fatansu ga sabon kakakin inda suka yi fatan Allah ya taya shi riko kuma yayi aiki da gaskiya da adalci

Ana saran nan da wasu 'yan sa'oi masu zuwa za'a rantsar da sabon kakakin majalisar dokokin ta Nijar