An dage zaben gwamnoni a Kaduna da Bauchi

Shugaban INEC, Parfesa Attahiru Jega
Image caption Shugaban INEC, Parfesa Attahiru Jega

Hukumar zaben Najeriya ta ce ba zata gudanar da zaben gwamnoni da na 'yan majalisar dokoki ba a jihohin Bauchi da Kaduna kamar yadda ta tsara yi a sauran jihohin kasar a ranar 26 ga wannan watan.

A cewar INEC din bisa dalilai na tsaro sai a ranar 28 ga wata za ayi zaben a jihohin Kaduna da Bauchi din.

Har wa yau hukumar INEC ta ce zata yi aiki da hukuncin kotu akan batun zaben gwamnoni a jihohin Sokoto da Kogi da Adamawa da Bayelsa da kuma Cross River.

Abinda hakan ke nufi shi ne sai a badi za a gudanar da zaben wadannan jihohin biyar.