An dage zaben Bauchi da Kaduna

Farfesa jega
Image caption Shugaban hukumar zaben Najeriya

Hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya ta dage zabukan gwamnonin jihohin Bauchi da Kaduna daga Talata ashirin da shida zuwa Alhamis ashirin da takwas ga watan Aprilu.

Dagewar ta biyo bayan tashe-tashen hankulan da aka yi fama da su a jihohin biyu biyo bayan sakamakon zaben shugaban kasar da aka bayyana cewa shugaba mai ci a yanzu Goodluck Jonathan na jam'iyyar PDP ne ya ci inda ya kada abokin takarar sa Janar Muhammadu Buhari na jam'iyyar adawa ta CPC.

Tashe-tashen hankulan wadanda suka auku a jihohin Najeriya da dama sun haifar da asarar rayuka da dukiyoyi da dama a yankin arewacin Najeriya.

Shugaban hukumar zaben Farfesa Attahiru Jega ya ce zabe ba zai yiwu a jihohin Kaduna da Bauchi ba a ranar Talata mai zuwa saboda matsaloli na tsaro, a don haka za a dage su da kwanaki biyu.

Sanarwar ta zo ne a ranar da shugaban Najeriyar Goodluck Jonathan ya sha alwashin cewa za a gudanar da zabe a dukkan jihohi talatin da shida na kasar.

A baya dai kotun daukaka kara ta ce ba za a gudanar da zabukan gwamna ba a wasu jihohi biyar na kasar saboda wadanda suke kan kujerar ba su kammala sabon wa'adinsu ba, sakamakon soke zabensu da kotunan zabe suka yi.

Attahiru Jega ya ce yana fatan dage zaben zai taimaka wajen kara samar da kwanciyar hankali a jihohin biyu.

Ba za mu saurara wa masu tada fitina ba

Image caption Jonathan ya ce gwamnati ba za ta lamunci tashin hankali ba

A karo na biyu tun bayan da aka bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben Shugaban kasar da aka gudanar ranar asabar din da ta gabata, Shugaba Goodluck Jontahan ya yi wa al'ummar kasar jawabi dangane da tashe tashen hankulan da suka biyo bayan bayyana sakamakon zaben.

Shugaba Goodluck Jonathan yace anyi zaben shugaban kasar cikin nasara, inda kuma ya jinjinawa hukumar zaben kasar, wacce yace ta samar da yanayi na gudanar da sahihin zabe.

Sai dai batun tashen tashen hankulan da suka biyo bayan bayyana sakamakon zaben shi ne wani batu da ya yi kane-kane a cikin jawabin nasa.

Shugaban dai ya yi tir da kashe kashen rayuka da kuma kone kasuwanni da wuraren ibadah, kazalika da yadda wasu suka nuna bijirewa ga shugabanni har ma da sarakuna in ji shi.

Shugaba Goodluck Jonathan ya kara da cewar yanzu tura ta kai bango. Yace gwamnati ba za ta lamunce da duk wani nau'i na tashin hankali ba.

Shugaban yace ya umarci hukumomin tsaro da su bi dukkanin hanyoyin da doka ta tanadar, domin kawo karshen tashe tashen hankulan dake aukuwa da gaggawa.

Yace ya umarci daukacin gwamnonin jahohin kasar dasu dauki cikakken nauyin kare lafiyar matasa masu hidimar kasa wadanda suma rikicin ya rutsa da wasunsu. Shugaba Goodluck yace za'a kafa wata hukuma da za ta gudanar da binciken musabbabin rikicin

Dr. Goodluck Ebele Jonathan ya kuma bayyana cewar zaben gwamnonin da aka shirya yi ranar Asabar yana nan daram.

Dangane da haka ne shugaban ya umarci mutane da su fito domin zabar mutanen da za su ciyar da kasa gaba.