Ba za mu saurarawa masu tayar da fitina ba - Goodluck Jonathan

Shugaban Najeriya, Dr. Goodluck Ebele Jonathan
Image caption A cikin jawabin da ya yi wa al'ummar kasar, Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya bayyana cewar gwamnati ba zata lamunce da duk wani nau'i na tashin hankali ba

A karo na biyu tun bayan da aka bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben Shugaban kasar da aka gudanar ranar asabar din da ta gabata, Shugaba Goodluck Jontahan ya yi wa al'ummar kasar jawabi dangane da tashe tashen hankulan da suka biyo bayan bayyana sakamakon zaben.

Shugaba Goodluck Jonathan yace anyi zaben shugaban kasar cikin nasara, inda kuma ya jinjinawa hukumar zaben kasar, wacce yace ta samar da yanayi na gudanar da sahihin zabe.

Sai dai batun tashen tashen hankulan da suka biyo bayan bayyana sakamakon zaben shi ne wani batu da ya yi kane-kane a cikin jawabin nasa.

Shugaban dai ya yi tir da kashe kashen rayuka da kuma kone kasuwanni da wuraren ibadah, kazalika da yadda wasu suka nuna bijirewa ga shugabanni har ma da sarakuna in ji shi.

Shugaba Goodluck Jonathan ya kara da cewar yanzu tura ta kai bango. Yace gwamnati ba za ta lamunce da duk wani nau'i na tashin hankali ba.

Shugaban yace ya umarci hukumomin tsaro da su bi dukkanin hanyoyin da doka ta tanadar, domin kawo karshen tashe tashen hankulan dake aukuwa da gaggawa.

Yace ya umarci daukacin gwamnonin jahohin kasar dasu dauki cikakken nauyin kare lafiyar matasa masu hidimar kasa wadanda suma rikicin ya rutsa da wasunsu. Shugaba Goodluck yace za'a kafa wata hukuma da za ta gudanar da binciken musabbabin rikicin

Dr. Goodluck Ebele Jonathan ya kuma bayyana cewar zaben gwamnonin da aka shirya yi ranar Asabar yana nan daram.

Dangane da haka ne shugaban ya umarci mutane da su fito domin zabar mutanen da za su ciyar da kasa gaba.