Ivory Coast za ta koma cikin kungiyar AU

Shugaban Cote D'Ivoire Allasane Ouattara Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaban Cote D'Ivoire Allasane Ouattara

Kungiyar Tarayyar Afirka AU ta ce ta janye dakatarwar da ta yiwa kasar Ivory Coast, tare kuma da soke takunkumin da ta sakawa kasar.

Wannan sanarwar ta nuna marhabin din da aka yi da Alassane Outtara, wanda ya yi nasara a gwagwarmayar iko tsakaninsa da abokin adawarsa Laurent Gbagbo.

Wani Direkta a kungiyar ta AU, El-Ghassim Wane, ya ce an dage haramcin nan take.

Ya ce a lokacin kwamitin zaman lafiya da tsaro ya yanke shawarar dakatar da Cote d'Ivoire daga duk wasu abubuwa da suka shafi kungiyar AU, har sai lokacin da shugaba Outtara zai hau mulki, kuma abinda ya faru kenan tun daga ranar 11 ga watan Aprilu.