Dakarun Ouattara sun yi artabu tsakaninsu

An ta tafka rikici a birnin Abidjan dake Kasar Ivory Coast a tsakanin dakarun da ke yiwa Shugaba Alassane Ouattara biyayya, wadanda suka karbe ikon birnin tun kimanin mako guda da ya gabata.

Fadan dai ya faru ne a tsakanin wata kungiya da ta kira kanta Invisible Commando, wadda ke rike da ikon wasu wurare na birnin na Abidjan, da kuma dakarun da Shugaban ya taho dasu daga arewacin kasar.

Wakilin BBC ya ce, harbe harben da aka yi a arewacin birnin Abidjan wanda aka shafe kasa da minti talatin ana yi, ya janyo fargaba a zukatan al'ummar Ivory Coast, kan cewa za'a samu matsalar rashin tsaro.