Japan ta haramta zama a wuraren tashar nukiliya ta Fukushima

Yankin tashar nukiliya ta Fukushima a kasar Japan Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Hukumomin Japan sun umarci mutanen da har yanzu ke rayuka a kusa da tashar nukiliya ta Fukushima, wacce girgizar kasa da kuma tsunami suka lalata dasu tattara ina-su- ina- su, su bar yankin.

Japan ta sake tsaurara matakan hana zirga zirga a murabba'in kilomita 20 daga tashar nukiliya ta Fukushima da ta lalace, inda ta haramta shiga yankin baki daya.

Fira Ministan kasar Japan Naoto Kan ne ya bayyana daukar wannan mataki a lokacin da ya kai ziyara kusa da tashar nukiliyar a arewa maso gabashin Japan.

Dokar dai za ta fara aiki ne da misalin karfe 3 na rana agogon GMT.

Wakilin BBC a Tokyo ya ce, gwamnati ta umurci mazauna yankin da su kauracewa yankin, bayanda girgizar kasa da tsunami suka lalata tashar nukiliyar, to amma saboda 'yan sandan kasar basu da hurumin tursasa wannan doka yasa wasu mutane suka sake dawowa domin cigaba da rayuwa a wannan yanki.