'Yan tawaye sun samu karin nasara a Libya

Wani dan tawaye a Libya Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wani dan tawaye a Libya

Rahotanni na nuna cewa dakarun 'yan tawayen kasar Libya sun karbe iko da yankin kan iyakar kasar da Tunisia ta bangaren yamma.

Hakan ya faru ne bayan wata arangama da dakarun dake biyayya ga Kanar Gaddafi.

Rahotanni na nuna cewar wasu daga cikin dakarun gwamnatin Libyar sun mika wuya ga hukumomin Tunisia.

Wannan shi ne karon farko da dakarun yan tawayen suka samu wata nasara ta dannawa gaba, a baya bayan nan.

Can kuma a garin Misrata, da aka yi ma kofar-rago, ana ta kokarin kwashe wadanda suka jikkata ne a sakamakon hare haren da ake kaiwa kasar ta libya.