An sake tsare jagoran 'yan adawar Uganda

Dr Kizza Besigye Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Jagoran 'yan adawar Uganda Dr Kizza Besigye

Ana ci gaba da tsare jagoran 'yan adawar kasar Uganda Kizza Besigye, bayan da aka tuhume shi da laifin shiga zanga-zangar da hukumomi suka haramta.

Wani alkali ya umarci a ci gaba da tsare shi har zuwa ranar Laraba, lokacin da za a saurari bukatar neman belin da ya gabatar.

Dr Kizza Besigye ya shirya wata zanga-zanga ce ta zuwa wuraren aiki da kafa.

Yau aka shiga kwana na hudu na zanga-zangar da 'yan adawa ke jagoranta domin kokawa da tsadar rayuwa.

Shugaban kasar Uganda Yoweri Museveni, ya ce ba zai kyale zanga-zangar ta 'yan adawar dake ikirarin cewa an tafka magudi a zaben da aka gudanar a kasar a baya bayan nan, ta ci gaba ba.