Dakarun Syria sun budewa masu zanga zanga wuta

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Akalla masu zanga zanga 200 ne suka mutu a makwanni da suka gabata

Rahotanni sun ce dakarun Syria sun budewa dubban masu zanga zanga wuta bayan sallar juma'a a yau.

Dubban masu zanga-zanga dai sun fito ne domin nuna adawa ga gwamnatin shugaba Bashar al-Assad.

Wani wanda ya gani da idanunsa ya ce akalla mutane uku sun raunata a kusa da Damascus a yayinda rahotanni ke nuni da cewa an budewa masu zanga-zanga wuta a Homs da kuma Hama.

A ranar Alhamis din da ta gabata ne dai Shugaba Assad ya dage dokar ta baci da aka sanyawa kasar na tsawon shekaru biyar.

Kungiyoyin kare hakkin bil'adama sun ce akalla mutane 200 sun rasa rayukansu a zanga-zangar da aka gudanar a kasar a makwannin da suka wuce.