Ana cigaba da bata-kashi a iyakar Cambodia da Thailand

Sojan kasar Thailand
Image caption An cigaba da bata-kashi akan iyakar kasashen Cambodia da Thailand

An ci gaba da bata-kashi a iyakar kasashen Thailand da Cambodia, kwana guda bayanda yaki tsakanin bangarorin biyu yayi sanadiyyar asarar rayukan sojoji shidda.

Dakarun sun yi musayar wuta a rana ta biyu.

Dubban fararen hula ne aka kwashe daga yankin, wanda ke da nisan kimanin kilomita dari daga yankin kudancin wurin bauta na Preah Vihear, inda aka yi bata-kashin na baya.