Kalubale ga Goodluck, hada kan kasa

Dattawa a Nijeriya na ci gaba da tofa albarkacin bakinsu dangane da tarzomar da ta biyo bayan zaben shugaban kasar da aka yi a ranar asabar da ta gabata, wadda ta yi sanadiyar hasarar rayuka da dukiya mai yawa. An dai yi wannan tarzomar ce a yankin arewacin kasar inda masu boren suka yi zargin cewa an murde sakamakon zaben na shugaban kasa, tare da hadin bakin wasu manya daga yankin na arewa domin baiwa Shugaba Goodluck Jonathan dan kudancin kasar, galaba a zaben.