Bam ya fashe a unguwar Rafinguza dake jahar Kaduna

Taswirar Najeriya Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Hukumar 'yan sandan jahar Kaduna ta tabbatar da tashin wani abu mai kama da bam a unguwar Rafinguza dake jahar Kaduna

Rahotanni daga jahar Kaduna na nuna cewa an sake samun fashewar wani abu mai karfin gaske, wanda ake kyautata zaton bam ne.

Bayanai na fari fari na nuna cewa bam din ya tashi ne a wata Unguwa da ake kira Rafinguza, wadda ke kusa da Unguwar da 'yan majalisar dokokin jahar kaduna ke zama, wato Legislative Quarters.

Tuni dai rundunar 'yan-sanda ta jahar Kadunan ta tabbatar da afkuwar wannan al'amari tare da tabbacin cewa ta cafke mutane ukku bisa zarginsu da hannu a tada bam din

Wannan ne dai karo na hudu da bama bamai ke tashi a jahar Kaduna.

Na fari dai ya tashi ne a lokacin da ake daf da fara zabe a kauyen Mahuta.

Na biyu dana uku sun tashi ne a unguwannin Kabala west dana Magajin gari ranar da za'ayi zaben shugabankasa.

Zaben shugabankasar dai shi ya haifar da rikice rikice a jahar ta Kaduna abinda yasa ma yanzu haka hukumar zaben kasar tace ta dage zaben gwamnonin da za'a yi a jahar daga ranar talata zuwa ranar alhamis din makon mai zuwa