'Yansanda a Kaduna sun kama mutane biyar

Hukumomi a jahar kaduna sun fara bincike dangane da Bom din daya tashi jiya a wata unguwa da ake kira Rafin Guza dake kadunan.

Abincike na fari dai hukumar ta gano wasu karin Bama baman da aka riga aka hada su har guda ukku,wadanda rundunar yansanda ta jahar kadunan tace ana shirin kaddamar da hare hare ne a wasu wurare a jahar,wadanda suka hada da wuraren ibada da gidajen mutane domin kokarin kara tada hankulan jama'a.

Baya ga Bama baman da aka samu a gidan da wannan Bam ya tashi dai, an kuma sami bindigogi ciki har da muggan bindigogin nan kirar AK 47 guda biyu, bindigogi kanana wato pistol da wasu makamai masu hadari kirar gida.

Tuni dai 2 daga cikin wadanda Bom din ya tashi dasu suka rasu.