Dubban 'yan Nijar sun shiga wani hali a Misrata

Amurka ta ce ta kai harinta na farko a kan Libya ta amfani da jirginn saman nan da bai da direba. Ba ta dai ba da karin bayani ba.

A halin kuma da ake cikin gwamnatin Libya ta ce za ta janye daga birnin Misrata bisa yawan barnar da ake wa jama'ar birnin.

Wani jami'in wata kungiyar ta kaurar mutane a duniya, IMO, ya ce akwai matsalar 'yan gudun hijira a birnin Misrata, inda yace yanzu haka a iya sanin akwai dubun-dubutar 'yan ci-rani, galibi daga Nijar, wadanda ke jiran a kwashe su."