Sakon Fafaroma kan bikin Easter

Fafaroma Benedict Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Fafaroma ya yi jawabi kan bikin Easter

Fafaroma Benedict ya ce rayuwa za ta kasance mara ma'ana idan aka ce dan Adam ya kasance ne a zaune kara-zube.

A sakonsa na jajiberan bukukuwan Easter, Fafaroman ya kara da cewa, rayuwar dan Adam na da matukar muhimmanci shi yasa Allah ya halicce shi mai tunani.

Ya ce ba daidai ba ne a ce halittar dan Adam ta bayyana ne haka kawai a wani bangare na duniya.

Fafaroman ya yi kira ga Kristoci da su hada kansu.