Muhawara kan dage zaben Kaduna da Bauchi

Shugaban hukumar zaben Najeriya, Attahiru Jega
Image caption Ana muhawara kan dage zabe a jihohin Kaduna da Bauchi

Masana kundin tsarin mulki a Najeriya na cigaba da tafka mahawara dangane da dage zaben da hukumar zaben kasar ta yi a jihohin Kaduna da Bauchi.

Yayin da wasu masana ke ganin cewa matakin da hukumar zaben ta dauka ya yi daidai, wasu na ganin kamata ya yi a gudanar da zaben a lokacin da aka samu kwanciyar hankali sosai a wadannan jihohi.

A cewar masu wannan ra'ayi, tsarin mulkin kasar ya bayar da damar dage zabe idan an samu barkewar tashen-tashen hankula, ko wani bala'i, zuwa lokacin da aka samu kwanciyar hankali.

Barista Yahya Mahmud na daga cikin masu son ganin an kara kwanakin gudanar da zaben.

Ya ce sashe na ashirin da shida na dokar zaben kasar ya bayar da damar dage zabe har tsawon wani lokaci idan aka ga cewa za a fuskanci tashin hankali yayin gudanar da shi.

Sai dai Barista Mike Ahamba ya ce, ba zai yiwu hukumar zaben ta dage gudanar da shi har tsawon fiye da wata daya ba, domin hakan zai yi karo da kundin dokar zaben kasar.