An kama 'yan adawa a Syria

Masu zanga zanga a Syria Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Masu zanga zanga a Syria

Rahotanni daga Syria sun ce an kama masu adawa da gwamnati gwammai, bayan zanga-zangar da aka yi jiya Asabar da ranar Jumma'a, inda aka harbe masu zanga-zangar fiye da dari.

Kungiyar Lura da Kare Hakkin bil Adama ta Syria ta yi Allah wadai da tsare mutane goma sha takwas da aka yi a arewacin kasar, da wasu gwammai a wasu wuraren, ta kuma nemi a sake su.

Ba A dai samu tabbacin kamen ba daga wata majiya ta daban.

Gwamnatin Biritaniya dai ta yi kira ga 'yan kasarta a Syriar da su fice saboda tabarbarewar da sha'anin tsaro ke yi a kasar.