Koma bayan da Arsenal ke fuskanta laifi na ne- Wenger

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kocin Arsenal Arsene Wenger

Kocin Arsenal, Arsene Wenger ya ce a dora masa duk wani laifi, sanadiyar koma bayan da kungiyar ke fuskanta a kakar wasan bana.

Kocin ya yi wannan furucin ne bayan da kungiyarsa ta sha kashi a hanun Bolton a gasar Premier ta Ingila, inda aka tashi da ci biyu da guda wanda kuma ya dakushe kokarin kungiyar na lashe gasar ta bana.

A yanzu haka dai Arsenal na bayan mai jagoranci a gasar ta Premier wato Manchester United da maki tara a yayinda wasanni hudu su ka rage mata a kakar wasan ta bana.

Idan har Manchester United ta doke Arsenal a filin Emirates a ranar lahadi, zai tabbata cewa Arsenal za ta kammala kakar wasan ta bana ba tare da daukan kofi ko guda ba.

"Gaskiya 'yan wasan mu sun taka rawar gani a kakar wasanni ta bana. Idan akwai wanda za'a daurawa laifi, ina ganin ni ne." In ji Wenger.

Wenger ya amince cewar dokewar da Bolton ta yiwa kungiyarsa ta dukushe duk wani kokari da kungiyar ke yi na lashe gasar Premier a bana.