Bama-bamai sun sake tashi a Maiduguri

'Yan sanda na duba wani abu da ake zato bam ne a Maiduguri
Image caption Bama-bamai sun tashi a Maiduguri

A Najeriya, wasu abubuwa uku da ake zaton bama-bamai ne sun tashi a unguwar Maduganari da ke birnin Maiduguri na jihar Borno. Bama-baman sun tashi ne a jiya da daddare.

Ko a dazu da misalin karfe tara na safiyar yau ma an sake samun tashin wani bam din a kusa da Kasuwar Shanu wanda shi kuma yayi sanadiyyar jikkatar dan sanda guda.

Birnin na Maidugurin ya jima yana fama da irin wadannan hare haren wanda tuni Kungiyar nan ta Boko Haram suka yi ikirarin suke da alhakin kaddamarwa.

Daya daga cikin bama-baman ya tashi ne a wata mashaya, kuma lamarin ya jikkata mutane da dama da aka garzaya da su zuwa asibiti.