Yau ake gudanar da zabe a kasar Chadi

Daga hannun hagu, shugaban Chad, Idris Deby Hakkin mallakar hoto xinhua

Yau Litinin ne al'ummar kasar Chadi za su kada kuri'a a zaben shugaban kasar.

Ana sa ran shugaba mai ci, Idris Deby zai lashe zaben da zai bashi damar yin wa'adin mulki na hudu.

Shi dai shugaba Idris Deby ya shafe kimanin shekaru ashirin akan karagar mulkin da ya dare ta hanyar juyin mulki.

Wadanda za su kalubalanci shugaba Deby a wannan zabe dai sun hada ne da wani lauya da kuma tsohon ministan aikin gona.

Sai dai kuma gaggan 'yan adawar kasar sun kauracewa zaben na yau, bayan sun kasa cimma bukatunsu na yin garambawul ga tsarin zaben kasar.