Sojojin Syria na kai hari a birnin Derra

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Masu zanga zanga

Daruruwan sojojin Syria ne tare da tankokin yaki suka yiwa birnin Derra kawanya, inda zanga-zangar kin jinin gwamnati ya yi kamari a kasar.

Masu adawa da gwamnatin kasar sun ce ana ta harbe-harbe a birnin kuma an kashe mutane da dama.

Rahotanni na nuni da cewa, dakarun kasar sun shiga wata unguwa dake wajen garin Damascus inda aka kame wasu mutane.

A makon da ya gabata dai Shugaba Assad ya dage dokar ta bacin da aka sanya da dadewa a kasar amma 'yan adawa sun yi watsi da matakin inda suka ce gwamnatin kasar ba ta da niyyar gyara a kasar.