Jami'an tsaro na artabu da masu zanga-zanga a Yemen

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Masu zanga zangar kin jinin gwamnati a Yemen.

Jami'an tsaro a Yemen sun budewa masu zanga-zangar kin jinin gwamnati wuta a kasar domin a tarwatsa su.

Masu zanga zangar dai na neman Shugaban kasar Ali Abdullah Saleh ya sauka daga kan mulki.

Wadanda suka ganewa idonsu sun ce an yi harbin kan mai uwa da wabi kuma an harba hayaki mai sa hawaye, inda suka ce akalla mutane goma sun raunana.

Masu zanga-zangar dai na adawa ne da shirin majalisar hadin gwiwar kasashen dake gabar tekun Gulf, inda suka baiwa Shugaba Saleh damar sauka daga kan mulki bayan wata guda da kuma kariya daga fuskantar tuhuma.

Hadakar kungiyoyin 'yan adawa dai sun ce sun yi watsi da yarjejeniyar da majalisar ta cimma.