An fara bincike kan Laurent Gbagbo

Tsohon shugaban Ivory  Coast, Gbagbo Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption An fara binciken Laurent Gbagbo

Shugaban Ivory Coast, Alassane Ouattara ya bayyana cewa, gwamnatinsa ta fara gudanar da bincike akan tsohon shugaba Laurent Gbagbo.

Za a gudanar da binciken ne dangane da zargin da ake yiwa Mista Gbagbo na take hakkin Bil Adama. Alassane Ouattara ya kuma fadawa gidan talabijin din gwamnati cewa, ana kuma bincikar dukkan mukarraban tsohon shugaba, Gbagbo.

Sai dai kungiyoyin kare hakkin bil'adama da ma majalisar dinkin duniya sun ce, dukkan bangarorin da suka hada da na Laurent Gbagbo da ma na Alasane Ouattara sun aikata kisa da kuma cin zarafin jama'a a kasar.