Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Haifi Ki Yaye da BBC Hausa: Ayyukan wanzamai kan jariri

Image caption Hukumar Lafiya ta duniya na nuna damuwa kan al'adun gargajiya

A al'ada irin ta malam Bahaushe, bayan mace ta haihu lafiya, kuma abinda ta samu ma na cikin koshin lafiya, akan gayyato wanzami don yin wasu abubuwa ga sabon jariri ko jaririya.

Yankan angurya na daga cikin abubuwan da sukan yiwa jaririya idan an kira su, kuma wannan al'adar a cewar Hukumar lafiya ta duniya WHO, al'ada ce da aka fi yiwa jarirai mata zuwa 'yan matan dake da shekaru goma sha biyar a duniya.

Inda hukumar ta bayyana cewa kimanin mata da yara mata miliyan 100 zuwa 140 ne ke tattare da matsalolin da yankan angurya ke janyowa a fadin duniya.

Tana mai cewa al'adar dai take hakkokokin mata da yara ne dake faruwa a kasa da kasa.

WHO ta kiyasta cewa a nahiyar Africa mata miliyan 92 ne da suka kama daga 'yan shekaru goma zuwa sama aka cirewa angurya.

Yayinda a duk shekara kimanin yara mata miliyan uku ne ke fuskanatar barazanar gamuwa da irin wannan al'adar a nahiyar.

Mun dai tattauna da masana domin jin irin illar da ke tattare da wannan al'ada.