Al Qaida ta nemi Faransa ta janye daga Afghanistan

Shugaban Faransa, Nicolas Sarkozy Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Shugaban Faransa, Nicolas Sarkozy

Kungiyar al Qaeda reshen Arewacin Afrika ta nuna wani faifan bidiyo dake dauke da hotonan wasu yan kasar Faransa, su hudu da aka sace a jamhuriyar Niger. A cikin faifan bidiyon mutanen da aka sace sun yi kira ga shugaban Faransa, Nicolas Sarkozy akan ya janye dakarun Faransa daga kasar Afganistan.

Sai dai gwamnatin Faransa ta yi watsi da wannan bukata.