An sabunta: 29 ga Aprilu, 2011 - An wallafa a 12:58 GMT

An daura auren William da Kate

13:50: Mun kawo karshen hoton bidiyo da bayanan da muke kawo muku kai tsaye kan yadda bikin Yarima William da Kate Middleton ya gudana. A yanzu dai an gama daurin aure, kuma ana can anan ci gaba da shagulgula - don haka sai ku kasance da mu a sauran shirye-shiryenmu na rediyo, ko kuma ta hanyar latsa wannan rariyar likaudin domin samun karin bayani. http://www.bbc.co.uk/hausa/indepth/royalwedding_cluster.shtml

13:47: A sakon da ya aiko mana ta email Abdulkadir Barthez Kangiwa jihar Kebbin Najeriya cewa ya yi, yanda birnin London ya cika ya batse a dalilin bikin auren Yarima Williams da Kate Middleton, Allah ya sa a watse lafiya.

12:49: A sakon da ya aiko mana ta email Abba Mati mai fata cewa ya yi, ina taya daukacin al'ummar Burtaniya dama BBC murnar daurin auren Yarima William da amaryarsa Kate Middleton.

12:43: Kamar yadda tsarin sarauta ya tanada, a wurin wannan bikin Sarauniya Elizabeth ta nada Yarima William a matsayin Duke na Cambridge. Yayin da amaryarsa ta zamo Duchess ta Cambridge.

12:27: Yarima William da amaryarsa Kate da kuma Sarauniya sun isa fadar Burkingham Palace.

12:15: Yarima William da matarsa Kate Middleton suna tafiya suna dagawa mutane hannu - yayin da jama'ar da suka taru suke ta shewa domin nuna farin cikinsu.

12:11: Sun fito sun hau keken doki na kasaita wanda zai dauke su zuwa fadar sarauniya inda za a gudanar da sauran bukukuwa.

12:08: Ga Yarima William nan ya rike hannun amaryarsa Kate Middleton suna zagaya majami'ar Westminster - inda suke murmushi kuma kowa da kowa na kallonsu.

12:02: A sakon da ya aiko mana ta email Kabiru Idris Pindiga cewa ya yi, irin shirye-shiryen da aka dade ana gudanarwa a fadin Burtaniya domin auren Yerima Williams, abune dake nuna girman muhimmancin da al'ada ke dashi a kasar.

11:58: A sakon da ya aiko mana ta BBC Hausa Facebook, Malami Bello cewa ya yi kai amma wannan kayataccen biki ya burge ni, nima na roki Allah ya nunamin nawa da amaryata Umma Usman, kuma ya fi na Yarima Williams duk wasu shuwagabanni ina so su sami halartarsa da sauran al'ummar duniya amin, su kuma Allah ya basu zaman lafiya amin.

11:48: A sakon da ya aiko mana ta email, Ibrahim Buba mai tureda Gashu'a cewa ya yi, Shugabannin Afrika ku yi koyi da Yarima William wajen dai dai ta talaka da mai Sarauta, domin samun saukin rayuwa.

11:42: A yanzu dai ana ta ci gaba da addu'o'i a majami'ar Westminster bayan daura auren Yarima William da Kate Middleton.

11:25: A sakon da ta aiko mana a shafin BBC Hausa Facebook Fatty Alfa cewa ta yi, wata miyar sai dai kaji a makwafta, mukam ba mu da wuta sai dai mukaranta muna biye da ku BBC.

11:21: A daidai wannan lokaci ne aka daura auren Yarima William da matarsa Kate Middleton.

11:19: Ga shinan ana daura auren Yarima William da kate Middleton - inda ango ya sanyawa amaryarsa zobe, wanda ke nuna sun amince da juna.

11:18 Amarya Kate tare babanta - haka shi ma ango Yarima Wlliam tare da kaninsa Yarima Harry - wanda kuma shi ne bababn abokin ango sun jeru domin shirin daura aure inda ake ta addu'o'i kafin a daura.

11:09: A sakon da ya aiko mana a shafin BBC Hausa Facebok Auwalu Geographer, cewa ya yi BBC ina taya ango da amarya murnar shagalin biki, sai munzo.

11:07: Amarya Kate tare babanta - haka shi ma ango Yarima Wlliam tare da babansa suna tawo wa domin shirin daura aure.

11:03: Amarya Kate Middleton ta iso majami'ar Westminster a wata motar kasaita, inda take tare da mahaifinta - tana sanye da fararen kaya, sannan ta rike wata koriyar filawa.

10:56: Fira Ministan Australia Julia Gillard ta iso wannan waje - duk da matsayin gwamnatinta kan gidan sarautar Burtaniya, ta ce ya kamata a ce ta halarta saboda an gayyace ta.

10:47: A yanzu haka sarauniyar Ingila Queen Elizabeth ta iso majami'ar Westminster domin halartar daurin auren jikanta Yarima William da Kate Middleton.

10:39: A yanzu haka tawagar gidan sarautar Burtaniya ce ke ci gaba da isowa wurin wannan daurin aure. Kuma muna saran isowar amarya Kate Middleton nan gaba kadan.

10:33: Jami'an tsaron sun kama mutane goma bisa laifuka daban-daban a kusa da fadar Buckingham Palace da Westminster Abbey.... Laifukan sun hada da shaye-shaye da sabawa ka'idojin wajen da mallakar makamai da kuma sata. Wannan ya sa adaddin wadanda aka kama kawo yanzu ya kai 109.

10:26: A yanzu mahaifiyar kate Middleton tana kan hanyar zuwa wajen daurin auren.

10:24: Yarima William ya isa majami'ar Westminster Abbey, inda za a daura masa aure da Kate Middleton, yana sanye da jar riga.

10:05: Domin ganin hotunan shirye-shiryen bikin da kuma wuraren da za a gudanar da bikin sai ku latsa wannan rariyar likau din: http://www.bbc.co.uk/hausa/multimedia/2011/04/110421_royalwedding_gallery.shtml

10:00 A sakon da ya aiko mana a shafinmu na BBC Hausa Facebook, Umar Sada, cewa ya yi babban goro sai magogin karfe, Yarima William ka kafa tarihi, domin ka nuna cewa da talaka da sarki duk daya ne.

09:57: A sakon da suka aiko mana a shafinmu na BBC Hausa Facebook, Mansoor Said da Hafizu Balarabe cewa suka yi muna taya angwaye da kuma David Beckham Murna.

09:47: Shahararren dan wasan kwallon kafar nan na Ingila, kuma tsohon dan wasan Manchester United David Beckham ya isa wannan wuri tare da matarsa Victoria, domin taya angwayen murna.

09:40: Kimanin baki dubu biyu aka gayyata, kuma da dama daga cikinsu sun riga sun halarci wannan wuri, cikinsu har da wakilan gidan Sarautar Morocco da na Saudi Arabiya da kuma Swaziland.

09:35: Dubban mutane ne suka shafe daren jiya a kan titin birnin London inda suke jiran kallon bikin sarauta mafi girma cikin shekaru talatin. Angon wanda jikan Sarauniyar Ingila ne, ya fito domin gaisawa da jama'a da kuma masu tayashi farin ciki.

09:26: Manyan baki daga sassan duniya daban daban sun fara halarta a majami'ar Westminster Abbey inda za a daura auren Yarima William da Kate Middleton.

19:20: Muna sanar da jama'a cewa sai karfe 10:45 sannan hoton bidiyon zai fara nuna kai tsaye kamar yadda ka'ida ta tanada.

09:16: Mun fara kawo muku bayanai kai tsaye kan yadda bikin gidan sarautar Burtaniya ke gudana tsakanin Yarima William da Kate Middleton, wanda ake gudanarwa a majami'ar Westminster Abbey da ke birnin London. Muna bukatar jin ra'ayoyinku kan yadda wannan biki ke gudana, ko ta adreshinmu na email a hausa@bbc.co.uk ko kuma BBC Hausa Facebook wanda za ku iya samu a shafinmu na bbchausa.com.

BBC navigation

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.