Saliyo na bikin cika shekaru hamsin

Shugaban Saliyo, Earnest Koroma
Image caption Ana bukukuwa a Saliyo

Kasar Saliyo na yin bukukuwan cika shekaru hamsin da samun 'yancin kai daga mulkin mallakar Burtaniya.

Yanzu haka dai ana ta yin bukukuwa a duk fadin kasar ta Saliyo, wadda har yanzu ba ta gama farfadowa daga mummunan yakin basasa ba, wanda ya zo karshe a shekara ta 2002.

Shugaban kasar ta Saliyo Earnest Bai Koroma ya ce, yanzu kasar tana cikin zaman lafiya, kuma 'yan kasar sun amince su rika zabar shugabanninsu ta hanyar dimukradiyya.

'Yan kasar dai suna ta yin fatan alheri a gareta, inda suke cewa babban burinsu shi ne gwamnati ta gina al'umma mai yalwa.