Bikin gidan sarauta: Syria ba za ta halarta ba

Syria Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Majalisar Dinkin Duniya ta yi Allah wadai da rikicin na Syria

Gwamnatin Burtaniya ta janye gayyatar da ta yiwa jakadan Syria zuwa bikin gidan sarautar Burtaniyar tsakanin Yarima William da Kate Middleton.

Biyo bayan kisan da dakarun Syria suka yi wa masu zanga-zangar adawa da gwamnati, Ofishin kula da harkokin wajen Burtaniya, ya ce bai kamata jakadan Syria ya kasance a wajen bikinba.

Wakilin BBC yace sakataren harkokin wajen Burtaniya William Hague, ya taka rawa wajen hana jakadan na Syria haduwa da sauran wakilan kasashe da suka hada da Zimbabwe da Koriya ta Arewa da ma Iran.

A halin da ake ciki kuma, kungioyin kare hakkin bil'adama a kasar ta Syria, sun ce akalla mutane 500 ne aka kashe sakamakon harin da jami'an tsaro suka kaiwa masu zanga-zanga a sassan kasar da dama.

Duka dai Majalisar Dinkin Duniya da Amurka sun yi Allah wadai da matakin da jami'an tsaron na Syria suka dauka kan masu zanga-zangar.