Harin bam ya hallaka mutane 15 a Morocco

Harin bam a Morocco Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Harin bam a Morocco

Akalla mutane 15 sun rasa ransu, a wani harin da ake jin na kunar bakin wake ne, wanda aka kai a babban dandalin birnin Marrakesh na kasar Morocco.

Akalla wasu mutanen 20 sun jikkata.

Wani da ya shaida lamarin ya gayawa BBC cewa, tashin bam din ya lalata wani gidan shan shayi mai cunkoson jama'a, a dandalin Jamaa el-Fnaa, inda masu yawon bude ido suka faye zuwa.

Yawancin wadanda suka hallaka 'yan kasashen waje ne.

Harin shi ne mafi muni a Moroccon a cikin shekaru takwas.