Yaki da cutar Polio a Jumhuriyar Nijar

Rigakafin cutar shan inna
Image caption Rigakafin cutar shan inna

A Jamhuriyar Nijar yau ne hukumomin kasar suka shirya wani zaman muhawara tsakanin kwararrun likotoci da kungiyoyi farar hula da na masu hannu da shuni har ma da kungiyoyin addinai domin fadakar da al'umar kasar game da illolin da ke tattare da cutar shan inna, wato Polio.

Hakan dai wani share fage ne na wata yekuwa ta tsawon kwanaki hudu da za a fara daga gobe kan yaki da cutar ta polio da ma wasu karin cutukan.

A kasar ta Nijar, duk da cewar ana samun ci gaba a yaki da cutar ta Polio, har yanzu akwai iyaye dake kin bada 'ya'yansu a yi masu riga-kafi.