An samu karin sakamakon zaben gwamnoni

Zaben Najeriya Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption An fitar da sakamakon zaben gwamnonin jihohin Zamfara da Filato da Niger da kuma jihar Kwara

Hukumar zaben Najeriya ta kammala fitar da sakamakon zaben gwamnoni da na 'yan majalisu da aka yi ranar talata a jahohin Kebbi da Zamfara.

A jihar ta Zamfara dai, hukumar zaben ta bayyana sunan Alhaji Abdul'aziz Yare na jam'iyyar adawa ta ANPP a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jahar, bayanda ya kada gwamna mai ci yanzu wato Alhaji Mahmud Aliyu Shinkafi na jam'iyyar PDP.

Rahotanni daga jahar Filato kuwa na cewar hukumar zabe a jahar ta bayyana gwamnan jahar mai ci, Jonah Jang na jam'iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jahar, inda mataimakiyarsa Pauline Tallen ta jam'iyyar Labour ta zo ta biyu.

To sai dai rahotannin na cewa akwai wakilan jam'iyyun adawa da basu sa hannu a takaddar sakamakon zaben ba.

A can jihar Niger dake arewa maso tsakiyar Najeriya kuwa, hukumar zabe a jahar ta bayyana Gwamna Mu'azu Babangida Aliyu na jam'iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar a karo na biyu.

Sai dai jam'iyyun adawa a Jihar da shaidun gani da ido sun yi zargin an tafka magudi a zaben, abinda jam'iyyar PDPn ta musanta.

A jihar Kwara mai makwabtaka da jihar Niger kuwa, kanwar gwamnan jahar mai ci, wato Sanata Gbemisola Saraki ce tasha kayi daga hannun dan takarar jam'iyyar PDP Alhaji Fatai Ahmed a zaben gwamnan