Shugaba al Bashir na Sudan ya yi gargadi game da yankin Abyei

Shugaba Omar al Bashir na Sudan Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Shugaba Omar al Bashir na Sudan

Shugaban kasar Sudan, Omar Al bashir ya yi gargadin cewa gwamnatinsa ba za ta amince da sabuwar kasar kudancin Sudan ba idan ta nace akan ita ce keda iko a yankin Abyei mai arzikin mai da ake takaddama akai.

Mr Bashir ya fadi haka ne a lokacin da yake gabatar da jawabi a gaban dubun dubatar magoya bayansa a wani taron gangamin siyasa a jihar kudancin Kordofan dake da iyaka da yankin na Abyei.

Ya ce idan aka samu wata taswira ko yunkuri na sa yankin Abyei a cikin kundin tsarin mulkin sabuwar kasar , ba zamu taba amincewa da sabuwar kasar ba .