UEFA na tuhumar Real Madrid da Barcelona

Hakkin mallakar hoto Reuters

Uefa na tuhumar Real Madrid da Barcelona bayan abubuwan da suka faru a wasan da kungiyoyin biyu suka buga a wasan kusa dana karshe a gasar zakarun Turai.

Har wa yau Hukumar Uefa za ta binciki kalaman da kocin Real Madrid, Jose Mourinho ya yi bayan wasan.

Tuhumar da ake yiwa Real ya ta'alaka ne kan jan kati da aka nunawa Pepe da kuma Mourinho da kuma dabi'ar da magoya bayan kungiyar su ka nuna a lokacin wasan.

Har wa yau Uefa za ta duba jan katin da aka nunawa mai tsaron gida Barca dake kan benci wato Jose Pinto a lokacin da aka tafi hutun rabin lokaci a wasan.

Real Madrid dai ta sha kashi ne a hannun Barcelona da ci biyu da nema a wasan.

Kungiyoyin biyu za su bayyana a gaban kwamitin da'a da ladabtarwa na Uefa a ranar 6 ga watan Mayu domin amsa tuhumar da ake yi mu su.