Ana zabe a jihohin Kaduna da Bauchi

Wata rumfar zabe a Niajeria Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Wata rumfar zabe a Niajeria

A Nijeriya, yanzu haka ana can ana gudanar da zaben gwamnoni a jihohin Bauchi da Kaduna, bayan dage zaben da aka yi da kwanaki biyu a jihohin sanadiyyar rikice rikicen addini da kabilanci da aka yi fama da su.

Rahotanni dai na nuna cewa zaben duk da ana gudanar da shi karkashin tsauraran matakan tsaro, yana tafiya yadda ya kamata, to amma babu fitowar jama'a sosai, kamar yadda aka gani a zabukan baya.

Can ma a jihar Bauchi, rahotani na nuna cewa babu fitowar jama'a sosai a zaben.

Akwai kuma rahotannin fara jefa kuri'a tun lokaci bai yi ba a wasu wurare, da kuma rahotannin amfani da kudi karara a rumfunan zabe domin sayen kuri'a musamman a yankunan karkara.

A dukannin jihohin biyu dai, jam'iyyar PDP ce ke mulki, amma tana fuskantar kalubale daga jam'iyyun adawa.