Shugaba Obama zai kai ziyara yankin Alabama

Ta'alin da mahaukaciyar guguwar tayi a Amurka Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Mutane kimanin 300 ne suka rasu a Alabama da wasu jihohin dake kudancin Amurka, sakamakon mahaukaciyar guguwar data abkawa kasar mafi muni a tarihi

Idan an jima a yau ne shugaba Obama na Amurka zai ziyarci yankin da yayi kaca -kaca sakamakon daya daga cikin mahaukaciyar guguwar nan mafi muni a tarihin Amurka.

Mutane kimanin dari ukku ne suka rasu a Alabama, da kuma wasu jihohin dake kudancin kasar.

Gwamnan Alabama Robert Bentley, inda ta'alin ya fi muni ya bayyana cewa idan ka shiga Tuscaloosa abin ya munana.

Ya kara da cewar abin da ciwo musamman saboda kaunar Tuscaloosa da yake yi kuma saboda shine gwamna.