An soke zaben kananan hukumomin Misau da Ningi a Bauchi

Zaben Najeriya Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Hukumar zabe a jahar Bauchi ta soke zabukan kananan hukumomin Misau da Ningi a zaben gwamna dana 'yan majalisun da aka gudanar

A Najeriya, hukumar zaben jihar Bauchi ta soke zaben da aka yi a kananan hukumomi guda biyu na jihar bisa zargin yunkurin tabka magudi.

Kananan hukumomin da aka soke zabukan su sune Misau da kuma Ningi

Hukumar zaben jahar ta kara bada dalilan soke zaben a wadannan kananan hukumomi wadanda suka hada da rashin bin ka'idar gudanar da zaben da kuma tsorata masu kada kuri'a dama sace akwatunan zabe

Ya zuwa yanzu dai hukumar zaben jahar bata fito ta bayyana cewar za'a sake zaben ba, ko kuwa a'a, ko kuma ma yaushe ne za a sake zaben idan harma za'a sake

Sai dai wakilin BBC a jahar Bauchin, Isha Khalid yace zai yi wahala ace ba a sake zabukan ba a wadannan kananan hukumomi, ganin irin mahimmancin kananan hukumomin da kuma la'akari da cewar zabuka ne da suka shafi 'yan majalisar dokokin jahar da kuma gwamna

Wakilinmu ya kara da cewar soke zaben wadannan kananan hukumomi zai iya kawo jinkiri wajen fitarda sakamakon zaben, a bangare guda kuma yace ana ganin zai iya kawo takaddama ta siyasa dama watakila ta fuskar doka ganin cewar dokar zaben shekara ta 2010 ta zayyana cewar ranar 28 ga watan Afrilun shekarar da ake ciki, ita ce rana ta karshe daya kamata ace an gudanar da zabe, domin bada dama a rantsar da gwamnoni da 'yan majalisunsu a ranar 29 ga watan Mayu mai kamawa

Zaben jahar Bauchin dai ya gudana ne cikin tsauraran matakan tsaro, inda aka samu karancin fitowar masu zaben.