Yau ake bikin Yarima William da Kate Middleton

Yarima William da amaryarsa Kate Middleton
Image caption Ana shirin gudanar da gagarumin bikin auren Yarima William da kuma Kate Middleton a tsakiyar birnin landan

Idan an jima a yau ne za'a daura auren jikan sarauniyar Ingila, Yarima William da Kate Middleton.

An shirya wani gagarumin biki a Birnin Landan wanda zai samu halaratar manyan baki daga sassan duniya daban daban

Mutane na ci gaba da kwarara tsakiyar birnin London, a hanyar da Yarima William da Kate Middleton zasu bi, nan da sa'oi kalilan wanda zai kai su inda za a daura masu aure a Westminster Abbey.

Dubban masu fatan alheri ne suka shafe dare domin ganin wucewar masu auren. Yarima William ya burge mutanen da suke zube a kan titi, inda yayi wata 'yar fitowa ta ba zata a daren jiya.

Rundunar 'yan sandan Landan ta ce, hafsoshinta fiye da dubu biyar ne za su yi aiki a yau.

An yi kiyasin kudin da wannan aiki na tsaro zai ci, ya kai dala million 11.