A shirye muke mu tsagaita wuta - Kanal Gaddafi

Shugaba Gaddafi na Libya Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaban Libya Mu'ammar Gaddafi yace a shirye suke a cimma yarjejeniyar tsagaita wuta da dukkanin bangarorin biyu zasu amince da ita

Shugaban kasar Libya Kanal Gaddafi yayi kiran da a tattauna tare da kungiyar kawance ta NATO domin su kawo karshen hare hare ta sama da suke kaiwa kasarsa.

A lokacin da yake jawabi kai tsaye ta kafar talabijin na kasar, Kanal Gaddafi yace, a shirye yake da a kulla yarjejeniyar tsagaita wuta, idan har dukkanin bangarorin biyu sun amince da ita.

Sai dai dan shugaba Gaddafin wato Saif al-Islam ya ce ba za su taba yin saranda ba.

Saif ya ce ko da za a ci gaba da yi masu ruwan bama bamai na tsawon ranaku 40 ko shekaru 40 ba za su taba mika wuya ba.

Ya kara da cewar 'ba za mu daga farar tuta ba, tutar da zamu daga ita ce koriya, in Allah ya yarda za mu yi nasara' in ji saif.