Gwamnonin PDP sun lashe zabukan gwamnonin Kaduna da Bauchi

Alamar Jam'iyyar PDP
Image caption Sakamakon zaben gwamnonin Jahohin Kaduna da Bauchi ya nuna cewar jam'iyyar PDP ta sake lashe kejurun gwamnonin jahohin biyu.

A Najeriya an kammala fitar da sakamakon zaben gwamnonin jahohin Kaduna da Bauchi wanda aka gudanar ranar 28 ga watan Afrilu.

A jahar Kaduna dai, hukumar zaben jahar ta bayyana Gwamnan jahar mai ci, Mista Patrick Ibrahim Yakowa a matsayin wanda ya lashe zaben da yawan kuriu'a bisa takwarorinsa na sauran jam'iyyu.

To sai dai tuni jam'iyyun adawa a jahar suka la'anci zaben, inda suka ce an tafka magudi a cikinsa

Jam'iyyun adawar dai sun zargi jam'iyyar PDP da amfani da jami'an tsaro domin tafka magudi a wasu sassan jahar, zargin da 'yan jamiyyar PDP suka musanta.

Jam'iyyar PDPn ta shaidawa BBC cewar babu kamshin gaskiya dangane da zarge zargen

A yanzu haka dai an sake tsaurara matakan tsaro a unguwannin da ake tunanin rikici zai iya barkewa a jahar ta Kaduna

Can ma a jahar Bauchi, hukumar zaben jahar ta bayyana sunan gwamna mai ci, Malam Isa Yuguda, na jam'iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar.

Hukumar zaben ta bayyana sunan dan takarar jam'iyyar CPC, Hon. Yusuf Maitama Tugga a matsayin wanda yazo na biyu.

An dai bayyana sakamakon zaben ne duk kuwa da cewar an soke zabukan wasu kananan hukumomi biyu a cikin jihar saboda zargin tabka magudi.

Akasarin wakilan jam'iyyun adawa a jahar Bauchin dai basu sanya hannu a takaddar sakamakon zaben ba, hasali ma dai sunyi watsi da sakamakon.

Tun ma kafin a bayyana sakamakon zaben, 'yan adawar sunyi korafin cewar jam'iyyar PDP ta tafka magudi, hatta wasu masu sanya idanu sun bayyana cewar sun lura da magudi karara, abinda yasa wasu daga cikinsu suka kasa boye rashin jin dadinsu

To sai dai jam'iyar PDP a jahar ta karyata wadannan zargen zargen, tana mai cewar kage ne kawai

An dai gudanar da zabukan gwamnonin jahohin biyu karkashin tsauraran matakan tsaro da kuma dokar hana takaita zirga zirga a jahohin biyu

Bisa dukkanin alamu dai za a cigaba da tada jijiyoyin wuya dangane da sakamakon zaben gwamnonin jahohin biyu