Rashin tsaro ya addabi al'ummar Damagaram

Taswirar Jamhuriyar Nijar Hakkin mallakar hoto bbc
Image caption Taswirar Jamhuriyar Nijar

Yanzu haka rashin tsaro na ciwa al'ummar Jihar Damagaram da ke jamhuriyar Nijar tuwo a kwarya.

Wadansu mutane ne dai da ba a san ko su wanene ba dauke da bindigogi ke tsare motoci suna kwace dukiyoyi, a wadansu lokutan ma su kan kashe matafiya.

Wannan al’amari dai ya sa wadansu direbobi da fasinjoji tsoron bin wadansu hanyoyin jihar.

Shugaban Kungiyar Direbobi na Jihar, Malam Askiya, ya ce rashin tsaro ne ummulhaba’isin wannan matsala.

“Babu tsaro a hanya, gaskiya; tunda jami’an tsaro ba sa sintiri.

“Tunda ba a sintirin, su kuma ’yan fashin suna yadda suke so.

“...Ba yadda za a yi a samu kwanciyar hankali a kasar nan...kowa tsoro ya ke ji ya fito: yanzu a ce karfe daya [na rana, amma] kasuwa ta watse?”

Sai dai jami’an tsaro a Jihar ta Damagaram sun shaidawa wakiliyar BBC cewa ko da yake mutane suna ganin gwamnati ba ta kula da matsalar ba, ta damu matuka, kuma tana nemo hanyar magance ta.