Masar za ta bude iyakar ta da Zirin Gaza

Mashigin Rafah Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mashigin Rafah

Gwamnatin mulkin sojan Masar ta ce a karshen makon nan ne za a bude iyakar kasar da yankin Zirin Gaza, wacce ta kasance a rufe tsawon shekaru hudu.

Masar din dai ta rufe mashigar ta Rafah ne tare da hadin kan Isra'ila bayan kungiyar Hamas ta karbe iko da yankin na Gaza a shekara ta 2007.

Bisa ga dukkan alamu dai wannan mataki ba zai yiwa Isra'ila dadi ba, amma kuma 'yan kasar ta Masar za su yi marhabin da shi.

Rufe iyakar dai na cikin matakan da suka jawo wa tsohon shugaban kasar, Hosni Mubarak, bakin jini.