Karshen duniya ya zo, inji wadansu Amurkawa

Harold Camping Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Harold Camping

Wadansu kungiyoyin addini a Amurka sun bayyana cewa yau ce rana ta karshe a duniya.

Hasali ma, a hasashensu, mai yiwuwa tuni har wasu sassan duniya sun sheka barzahu.

Kungiyoyin, wadanda suka samo asali a California, sun kwashe watanni suna kashe makudan kuadade don yada wannan sako a fadin Amurka da ma sauran kasashen duniya.

Wata tashar radiyo a birnin na California, Family Radio, wadda wani dan shekaru tamanin da tara mai suna Harold Camping ya kafa ta yi ta yada wannan hasashe.

Shi dai Mista Camping ya yi imani cewa yau din nan karshen duniya zai zo.

“Ni da ku”, in ji Mista Camping, “muna rayuwa a karshen zamani.

“Za a yi wata gagarumar girgizar kasa wadda za ta sa girgizar kasar da aka yi a Japan ta zama tamkar wasan yara”.

Mista Camping yana da mabiya, wadanda suka rika shiga sako-sako a Amurka suna rabawa mutane kasidu.

Sun kuma yi imani cewa hasashen Mista Camping gaskiya ne saboda ya samo shi ne daga wasu lissafe-lissafe a cikin littafin Baibul.

Masu wannan yekuwa dai sun kashe makudan kudi wajen lillika daruruwan fostoci a fadin Amurka da ma wadansu kasashen duniya.

Sai dai ba wannan ba ne karo na farko da Mista Camping ya yi irin wannan hasashe—a shekarar 1994 ma ya yi, amma bai tabbata ba.