Taro kan yaki da ta'addanci

Wasu daga cikin Turawan da 'yan Alka'ida a Maghreb suka kama Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wasu daga cikin Turawan da 'yan Alka'ida a Maghreb suka kama

Ministocin harkokin waje na kasashen Mali, da Nijar, da Mauritaniya, da kuma Aljeriya na wani taro yau a Bamako, babban birnin kasar Mali, domin tattaunawa a kan sha'anin tsaro a yankin kasashen Afrika ta arewa, watau Maghreb.

Taron dai yana mayar da hankali ne musamman wajen duba matakan da suka dace wadannan kasashen su kara dauka, domin yaki da ayyukan ta'addanci kamar hare-hare, da awon gaba da Turawa da 'ya'yan kungiyar Alka'ida reshen Maghreb din ke yi a yankin.

A yanzu haka dai kungiyar ta Alqa'ida reshen Maghreb din na tsare da wasu turawa hudu 'yan kasar Faransa da suka sace a Nijar a bara da kuma wani dan Italiya da aka yi garkuwa da shi a Algeria a watan Fabrairu.

Ire-iren wadannan al’amura ne suka sa kasashen duniya jefa sunan Nijar a jerin kasashen Yamma da ba su da tabbas ta fuskar tsaro.